Gwamnatin Tarayya ta haramta sayar da naman daji a matsayin rigakafin hana yaduwar.

Wannan dai ya biyu bayan samun mutane 6 da suka harbu da cutar a kasarnan cikin wannan watan, kawo yanzu dai mutane 21 ne suka harbu da cutar a kasar nan cikin watan da muke ciki.

Masana sun ce akwai yiyuwar kamuwa da cutar ta hanyar cin naman dabbar da ta kamu da cutar, sai dai ba shine mafi yawan hanyar yaduwar ta ba.

Kwayar cutar ta monkeyfox wato kwandar Biri mai saurin yaduwa, tana bazuwa a Najeriya, galibi a wurare masu kusanci da dazuzzuka.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce Najeriya na fama da masu dauke da cutar a lokaci-lokaci tun bayan bullar cutar a shekarar 2017. An gano cutar musamman a kudancin kasar amma tun daga shekarar 2020, ta yadu zuwa tsakiya, gabashi da arewacin kasar.

A cewar masana kiwon lafiya, sunce galibi kananan dabobin da dake cin ciyawa ne ke yada cutar, a yayin da aka ci ko kuma aka taba su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: