DCP abba kyari ya goge rubutun da ya kawo rudani

0 62

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, ya goge wani rubutu da ya wallafa a Facebook inda ya bayyana alakar sa da wanda ake zargi da damfara ta intanet, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Hushpuppi ya ambaci Abba Kyari, a matsayin wanda ya karbi wani bangare na kudaden zamba wanda ake tuhumarsa a Amurka.

Abba Kyari ya shiga shafin sa na Facebook inda ya wanke kansa.

A bayanin da ya wallafa a Facebook, Abba Kyari ya ce bai nemi kudi daga Hushpuppi ba. Sai dai, ya ce ya gabatar da wanda ake tuhuma ga mai sayar da kayan sawa wanda Hushpuppi ya biya kusan naira dubu 300.

An ba da rahoton cewa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ya gyara bayanin nasa na Facebook sau da yawa kuma ya goge inda ya yi ikirarin cewa ya danganta Hushpuppi da mai sayar da kayan sawa.

‘Yan awanni kadan bayan gyara bayanin, sai aka goge shi gabadaya daga shafin sa, lamarin da ya jawo karin zargi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: