Jama’atul Nasrul Islam ta kammala shirin dashen bishiyoyi dubu 120 a fadin jihar Jigawa

0 119

Reshen Jihar Jigawa na Jama’atul Nasrul Islam ta kammala shirin dashen bishiyoyi dubu 120 a fadin jiharnan, zuwa karshen shekararnan.

Sakataren Jama’atu na jihar, Muhammad Babangida, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse cewa hakan wani bangare ne na aikin dashen bishiyoyi na kungiyar na shekara-shekara domin magance kwararowar hamada a jiharnan.

Ya kuma ce bishiyoyin zasu kare muhalli da kuma kayata shi, tare da samar da inuwa da abincin dabbobi.

Sakataren yace dukkanin cibiyoyin reshen jama’atu na kananan hukumomi 27 na jihar, za su shuka bishiyoyin.

A cewarsa, za a kuma a raba irin bishiyoyin ga manoma da sauran daidaikun mutane masu bukata domin shukawa a gonaki da gidajensu.

Muhammad Babangida ya gargadi mutane da su kauracewa sare bishiyoyi, babu gaira babu dalili.

Leave a Reply

%d bloggers like this: