Shugaba Mohammed Bazoum ya bai wa gwamna Zulum lambar girmamawa

0 141

Shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum ya bai wa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, lambar girmamawa ta kasa mai suna “de Grand Officer dans I`Ordre” sakamakon irin rawar da ya ke takawa a yaki da matsalolin rashin tsaro.

Shugaba Bazoum ya ce girmama Zulum ya zama wajibi idan aka yi a’akari da namijin kokarin da Zulum ke nunawa wajan yakar Boko Haram, damuwar da yake nunawa kan ‘yan gudun hijira da kokarin sake tsugunar da su a yankunansu da yaki ya lalata

An gudanar da bikin karrama Zulum ne a birnin Zinder, a wani bangare na bikin ranar yanci da Nijar ke gudanawar a ranar Talata 3 ga watan Agustan 2021.

Wannan shi ne karo na farko da wani shugaba a Nijar ke bai wa gwamna a Najeriya irin wannan lambar girmamawa. Zulum ya je Nijar din ne da rakiyar Sanata kashim Shettima da dan majalisa Mohammed Ali Ndume da kakakin majalisar jihar Borno Mohammed Tahir Monguno da wasu kwamishinoninsa.

Kafin hakan dai Gwamna Zulum ya zabi mazajen mafarauta 1000 domin kare manoma daga Boko Haram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: