Yadda hukumar DSS ta kama wasu da ake zargin sune sukayi Garkuwa da wani yaro dan shekara 6

0 80

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa DSS ta kama wasu da ake zargin sune sukayi Garkuwa da wannan yaron dan shekara 6 da haihuwa mai suna Abdullahi Salisu.

Kwamandan hukumar ta KANO Muhammad Salisu ne ya bayyana hakan ga manema laabarai a jiya Talata, inda yace masu laifin wandanda shekarunsu basu wuce 16 zuwa 21 ba, ansamu nasarar kamasu ne a wurin da sukace a jiye musu kudin fansa.

Kafin hakan dai anyi Garkuwa da wannnan yaron ne a ranar 16 ga watan yuli na wannan shekarar.

A cewar hukumar ta DSS ansace yaron da hadin bakin kawun yaron mai suna Abdulhadi Ibrahim.

A cewar hukumar masu Garkuwa da yaron sunhada baki ne da wasu masu tuka babur din adaidata sahu, masu suna Yusuf Abubakar and Adamu Shehu, domin daukar kudin fansar a wurin da suka nemi a ajiye musu kudaden.

Leave a Reply

%d bloggers like this: