EFCC Ta Kama Wasu Mutane 33 Bisa Zargin Aikata Laifukan Intanet A Jihohin Kwara Da Borno

0 407

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a yunkurinta na dakile yawaitar laifukan damfarar intanet a tsakanin matasa, ta kama wasu mutane 33 da ake zargi da aikata laifukan intanet a Ilorin babban birnin jihar Kwara da Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

A cewar Wilson Uwujaren, an kama 20 daga cikin wadanda ake zargin ne a Ilorin, yayin da sauran 13 da ake zargin an kama su a Maiduguri.

Kakakin na EFCC ya bayyana cewa, kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da nau’ikan wayoyi daban-daban da kwamfutoci da manyan motoci.

Wilson Uwujaren ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave A Reply

Your email address will not be published.