EFCC Ta Tura Jami’anta 100 Dauke Da Makamai Domin Yaki Da Sayen Kuri’u A Kano, Katsina Da Jigawa

0 171

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta tura jami’anta 100 dauke da makamai domin yaki da sayen kuri’u a jihohin Kano, Katsina da kuma Jigawa a zaben cike gurbi da ake yi na yau a jihohin.

Kwamandan EFCC na shiyyar Kano Farouk Dogondaji ne ya bayyana hakan a Kano ranar Juma’a.

Ya kuma bayyana cewa an kuma tura isassun ma’aikata domin sanya ido kan aikin zaben na mazabar Tudun Wada/Doguwa, da mazabar Takai, da kuma wasu zabukan ‘yan majalisar dokokin jiha a jihar Kano.

Dogondaji ya ce an kuma tura wasu jami’ai a zaben ‘yan majalisar dokoki a Katsina da Jigawa, domin hana sayen kuri’u.

Ya ce tura dakarun na daga cikin kudirin hukumar na tabbatar da sahihin zabe a yankunan.

Leave a Reply