Fada ya kaure a titunan Kyiv; babban birnin kasar Ukraine.

Hakan yazo cikin wata sanarwa da gwamnatin birnin ta fitar inda kuma ta gargadi mazauna garin da kada su tunkari haraba tagogin gidajensu.

A halin da ake ciki, rahotanni dake zuwa na cewa ana harba makamai masu linzami a Ukraine daga tekun Bahar Rum.

Ana kuma samun rahotannin kai hare-hare ta sama a yankuna da dama, lamarin dake nuna ta’azzarar yakin.

Sai dai kuma rundunar sojin Ukraine ta wallafa wani bayani inda ta yi ikirarin asarar da Rasha ta yi.

A cewar wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, an kashe sama da sojojin Rasha dubu 3 da 500 da ke da hannu a mamayar tare da kama kusan 200 a matsayin fursunonin yaki.

Sojojin na Ukraine sun kara da cewa Rasha ta kuma yi asarar jiragen sama 14, da jirage masu saukar ungulu 8, da kuma tankokin yaki 102 ya zuwa yanzu.

Kawo yanzu dai Rasha ba ta ce uffan game da ikirarin na Ukraine.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: