Labarai

Fadar shugaban kasa ta nisanta shugaba Buhari da shirin tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar jam’iyyar APC

Fadar shugaban kasa ta nisanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da shirin tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.

Majiyoyin fadar shugaban kasar sun bayyana hakanne a karshen makon jiya, inda sukace shugaba Buhari, wanda ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin marar nasara a wata hira da yayi da wani gidan talabijin.

Buhari ba zai iya goyon bayan duk wani yunkuri na tsaida toshon shugaban kasa Jonathan a matsayin dan takarar shugabancin kasa a zaben 2023 ba.

Wannan na zuwa ne bayan, an zargi guda cikin hadiman shugaban kasa Buhari, da saka photunan Jonathan a gaba-gaba, dake nuni da cewa, watakila Buhari ya goyi bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Amma, Fadar shugaban kasar ta kara tabbatar da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bayyana wanda yake marawa baya ba a zaben fidda gwani na shugaban kasa a tutar jam’iyyar APC ba.

Sai dai an yi ta rade-radin cewa Jonathan ne akafi ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai marawa baya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: