Wasu Yan bindiga sun kashe wani malamin makaranatar gaba da sikandire da ke Lafiya babban birnin jihar Nasarawa

0 69

Wasu Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani malami mai suna Zakari Kigbu wanda kafin rasuwarsa yana aiki da kwalejin kimiyya da fasaha ta Isa Mustapha Agwai da ke Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da ‘ya’yansa mata biyu a yayin harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan sandan jihar Rahman Nansel ne, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a yau.

Ya ce, sun samu kiran waya da misalin karfe 12:20 na safe game da harin hakanne yasa suka suka tattaro tawagarsu ta sintiri da sojoji zuwa wurin.

Da isar su, suka gano cewa an harbi Malamin a cikinsa, daga bisani ya mutu bayan an kai shi asibiti domin yi masa magani.

Nansel ya kara da cewa rundunar ta fara farautar wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: