Fadar shugaban kasa tayi watsi da rahoton EU kan zaben 2023

0 182

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) game da sakamakon babban zaɓen 2023 da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban ƙasa.

Cikin rahoton nata, ƙungiyar ta ce sunan hukumar zaɓen Najeriya INEC ya ɓaci, musamman saboda gazawa wajen ɗora sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a shafin intanet bayan ta yi alƙawari tun da farko.

Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana rahoton a matsayin maras kan-gado da aka haɗa shi ta hanyar dogaro da abubuwan da suka faru a rumfunan zaɓe 1,000 cikin 176,000 da aka kaɗa ƙuri’a a ranar zaɓen na watan Fabrairu.

A cewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake, ya bayyana Babban zaɓe na 2023, musamman na shugaban ƙasa wanda Bola Ahmed Tinubu ya lashe, shi ne mafi inganci da zaman lafiya da aka taɓa yi a kasar nan tun shekarar 1999.

Kazalika, ya ce babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da ƙungiyar Tarayyar Turai ko wata ƙungiyar ƙasar waje da ta gabatar da za ta yi fatali da ingancin zaɓen na watan Fabrairu, yana mai cewa sauran ƙungiyoyi kamar na rainon Ingila, Commonwealth, da Ecowas, da NBA sun yabi adalci da yadda aka gudanar da zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: