Farfesa Charles Soludo na Jam’iyar APGA ya lashe zaben Gwamnan Jihar Anambra

0 105

Farfesa Charles Soludo na Jam’iyar APGA ya lashe zaben Gwamnan Jihar Anambra, a zaben da akayi bayan ya samu nasara a Kananan Hukumomi 19 daga cikin 21 da suke Jihar.

Jami’ar Tattara Sakamakon Zabe ta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa Farfesa Florence Obi, ita ce ta sanar da sakamakon a yau da safe.

Yan takarkarun Jam’iyar PDP Mista Valentine Ozigbo da na Jam’iyar YPP Sanata Ifeanyi Uba, sun lashe zabe a Kananan Hukumomi dai-dai.

Amma dan takarar Jam’iyar APC Sanata Andy Uba, bai samu damar lashe zaben koda karamar hukumar 1 ba.

Mista Soludo dan shekara 61 a Duniya, wanda kuma shine tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, ya samu kuri’u dubu 112,229 fiye da abokin karawarsa na Jam’iyar PDP.

Dan takarar Jam’iyar PDP Mista Ozigbo ya samu Kuri’u dubu 53,807 sai kuma Sanata Andy Uba inda ya samu kuri’u dubu 43,285, sai kuma Ifeanyi Uba wanda ya samu kuri’u dubu 21,261.

Leave a Reply

%d bloggers like this: