Farfesa Maqariy ya ajiye aikin Jami’a

0 321

Bayan kwashe shekaru yana aikin koyarwa a Jami’ar Bayero dake Kano, babban limamin masallacin birnin tarayya dake Abuja Farfesa Ibrahim Ahmad Said Maqariy (Hafizahulla) ya ajiye aikinsa domin maida hankali wajen hidimtawa Addini.
Bayan Jami’ar ta Bayero ta amince da ajiye aikin malamin, a wata takarda dake dauke da amincewar hukumar makarantar.

Malam Maqarin ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin yana daya daga cikin mafarkinsa tun bai wuce Shekara Ashirin ba,yake fatan ya daina aikin gwamnati.

Sai a wannan Shekarun Allah Ya karbeshi a matsayin Mai cikakken yiwa addini hidima da Ma’aikatan Addini.

Inda ya kara da cewa Koda yake kowa da yanda Allah Ya tsara masa rayuwarsa, ba ya nufin wadanda ba haka ba ya fisu.

Maqari “Alhamdulillah da na bar Aikin Albashi da Kaina da Qarfina. Allah Ya Albarkaci abinda zai biyo baya na”

Leave a Reply

%d bloggers like this: