Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa ya umarchi maikatrar Lafiya karkashin kwaminshinan Lafiya Dr. Abba Zakari Umar dasu tantance yara 60 Yan asalin jihar Jigawa masu sha’awar karatun likita wato medicine domin gwamnati ta dauki nauyin su zuwa karatu kasar waje.
Za a dauki yara biyu daga kowacce mazabar dan majalissa.
Ana bukatar yara Yan kasa da 23, wadanda suke da a kalla credit 5 a Biology, Chemistry, Physics, English da mathematics.
- Tsawa ta salwantar da akalla gidaje 46,000 da makarantu, da dabbobi 700,000 a Vietnam
- Hukumar NEMA ta fara aikin agajin gaggawa a Maiduguri
- Tinubu ya jajantawa al’umar Maiduguri da ambaliyar ruwa ta shafa
- Akalla mutane 40 ne suka mutu a wani harin atilari kan wata kasuwa a Sudan
- Kwamitin majalisar Wakilai ya gayyaci shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma
Wannan shiri na yayan talakawa ne kawai wadanda suka gama karatun secondary a makarantun gwamnati kuma za a zakulo yaran bisa chancanta kawai.
Ana bukatar daukar a kalla mata 30, maza 30.
Duk me sha’awa yakai takardunsa ofishin kwamishinan lafiya na Jigawa Dr. Abba Zakari Umar daga ranar Juma’a 3rd July.
Kwamishinan lafiya na jihar Jigawa Dr. Abba Zakari Umar yace za’a rufe karbar takardun ranar 10 ga July a kuma yi jarrabawar tantancewa ranar litinin 13th July 2020.