Fiye da mutum 22 sun mutu a wani hari da aka kai a sansanin ‘yan gudun hijira a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango

0 80

Akalla mutane 22 ne suka mutu a wani hari da aka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke lardin Ituri a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

An dora alhakin harin kan kungiyar ‘yan tawaye dake dauke da makamai da aka ce sun bude wuta a sansanin.

An binne mutane 20 nan take a kaburbura guda biyu, yayin da wasu biyu kuma aka binne su daga baya.

Wani hari da aka kai a sansanin a makon da ya gabata ya kashe mutane 29.

An sanya dokar ta baci a Ituri da lardin Arewacin Kivu a ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata, domin hukumomi su shawo kan matsalar rashin tsaro a yankin da kungiyoyin masu dauke da makamai suka haddasa.

A wani bangare na dokar ta bacin, jami’an soji sun maye gurbin jami’an fararen hula da ke shugabantar yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: