Sabon jirgin yakin rundunar sojin Najeriya na Super Tucano ya tarwatsa mayakan ISWAP a jihar Borno

0 128

Sabon jirgin yakin rundunar sojin Najeriya na Super Tucano ya tarwatsa mayakan ISWAP tare da lalata motocinsu na igwa a garin Gajiram da ke jihar Borno.

Kafar yada labaran PRNigeria ta ce masu tayar da kayar bayan sun shiga garin a cikin motocin yaki da zummar kai masa hari, sai jirgin yakin ya isa wajen.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kwato makamai da dama a yayin da dakarun sama da na kasa suka fatattaki mayakan.

PRNigeria ta ce wani jami’in leken asiri na soja, ya ce akalla an ga gawarwarki 26 na mayakan bayan hare-haren saman.

A watan Yuli ne gwamnatin tarayya ta karbi jiragen yaki samfurin Super Tucano da ta saya a hannun Amurka da nufin yaki da matsalar rashin tsaro.

Jirgin Super Tucano yana aikin tattara bayanan sirri da sa ido da kai harin sama da kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: