Rundunar Ƴansandan Najeriya tana cigana da neman matasa masu sha’awar shiga aikin kuratan ƴansanda

0 155

Rundunar Yan sandan Najeriya ta ce tana neman Matasa masu sha’awar shiga aikin kuratan yan sanda.

Kakakin Rundunar yan sanda na Kasa CP Frank Mba, shine ya sanar da daukan yan sandan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

CP Frank Mba, ya ce an bude shafin daukan kuratan yan sandan ne daga yau 29 ga watan Nuwamba, kuma za’a rufe shafin a ranar 10 ga watan Janeru na sabuwar shekara.

Haka kuma ya ce daga cikin sharadan neman aikin dole ne Matasan da zasu nemi aiki su mallaki Lambar katin dan kasa wato NIN da kuma Asusun Email.

A cewarsa, yan Najeriya kadai suke da damar shiga aikin, kuma ba’a bukatar dan kasa da shekaru 17 ko kuma sama da 25.

CP Frank Mba, ya ce za’a iya ziyartar shafin na neman aikin  na www.policerecruitment.gov.ng

Kazalika, ya ce za’a gayyaci matasan da aka dauka aikin zuwa wurin tantancewa daga ranar 10 zuwa 24 ga watan Janeru na shekarar 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: