Kimanin Sojoji 2 sun mutu bayan karanbattar da sukayi da ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a jihar Borno

0 175

Kimanin Sojoji 2 ne suka mutu, biyo bayan karan battar da akayi dasu da Kungiyar Boko Haram da ISWAP a Jihar Borno.

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Soji Brigadier General Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

A cewarsa, sojoji sun yi nasarar kashe mayakan a wani hari da suka kai musu a karamar hukumar Gajiram Nganzai ta Jihar Borno a jiya Lahadi.

Kakakin rundunar ya ce nasarar da Sojojin suka samu, hadin gwiwa ne tsakanin Sojojin Sama da na Kasa wanda suke aiki karkashin rundunar Operation Hadin Kai.

Haka kuma ya ce sojojin sun yi nasarar kwato wasu kayayyaki da makamai daga hannun yan kungiyar ta Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas.

A jawabinsa, Shugaban Soji Lieutenant General Farouk Yahaya, ya bukaci sojojin su ninka kokarinsu wajen ganin cewa sun kame sauran mayakan da suka gudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: