Wasu ƴanbindiga kuma masu garkuwa da mutane sun harbi Kwamishinan Muhalli na Jihar Kogi

0 183

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu Garkuwa da mutane ne sun harbi Kwamishinan Muhalli na Jihar Kogi Hon Adewale Omofaiye.

Wasu majiyoyin sun ce yan bindigar sun kaiwa kwamishinan hari ne a lokacin da suka yiwa hanyar Kwantan bauna, inda kuma suka yi garkuwa da mutane da dama.

An bayar da labarin cewa lamarin ya faru ne a jiya da yamma a tsakanin Ikoyi da Iyara na karamar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi.

A lokacin da lamarin ya faru Kwamishinan yana kan hanyarsa ta zuwa Lokoja babban birnin Kwara, inda yan bindigar suka budewa motarsa wuta, tare da harbinsa a kafa.

Haka kuma an rawaito cewa Kwamishinan ya yi nasararkubuta ba’a sace shi ba, wani shaidar gani da ido ya ce amma yan bindigar sun sace wasu mafiya a hanyar tare da tafiya dasu zuwa cikin daji.

Kawo yanzu kwamishinan yana cikin wani kyakkyawan yanayi bayan samun kulawar likitoci.

Shugaban Karamar hukumar Ijumu Hon Isah Taufiq, ya umarci yan bijilanti da sauran Mafarauta su shiga dajin domin kubutar da sauran wadanda aka sace din.

Leave a Reply

%d bloggers like this: