Gwammatin jihar Jigawa ta amincewa da karbo bashin kudi naira miliyan dubu 18 da miliyan 700 daga gwamnatin tarayya

0 80

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amincewa bangaren zartarwa, karbo bashin kudi naira miliyan dubu 18 da miliyan 700 daga cikin kudi naira miliyan dubu 756 da gwamnatin tarayya ta amince a baiwa jihohin kasar nan bashi.

Mataimakin bulaliyar majalisar, Alhaji Bala Hamza Gada kuma wakilin mazabar Kazaure ya bayyana hakan a zaman majalissar na jiya.

Yace gwamnatin tarayya ta amince da baiwa gwamnatocin jihohin kasarnan bashin ciki har da jihar Jigawa, domin basu damar biyan basukan da ake bin su a baya, ba tare da samun gibi daga cikin kason su na wata-wata ba.

Ya ce za’a biya bashin ne cikin 30, kuma gwamnatocin jihohi zasu fara biyan bashin a shekaru 2 masu zuwa.

Shima da yake nasa jawabin shugaban masu rinjaye na majalisar kuma wakilin mazabar Maigatari, Habu Muhammad Maigatari ya ce kudaden zasu taimaka wajen cike gibin da ake samu daga kason arzikin kasa na wata wata dake zuwa jihoshi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: