Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kofar Damascus da titunan da ke kewaye a gabashin birnin Kudus rana ta biyu a jere yayin hutun Falasdinawa na bikin maulidin Annabi Muhammad (SAW).

Lamura sun kara rincabewa a yankin, jiya da yamma lokacin da sojojin mamaya na Isra’ila suka jikkata Falasdinawa 49 tare da kame wasu 10.

A jiya da yau, an gudanar da bukukuwan iyalai da yara a kofar Damascus, daya daga cikin wuraren jama’a da Falasdinawa a birni ke taruwa, don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi.

Hotuna da bidiyo da aka dinga yadawa sun nuna yadda sojojin Isra’ila suka kame matasa tare da kai musu hari a jiya, suna dukan masu wucewa da sanduna, da bin bayan yara, da wawashe kayyaki a shagunan dake babban titin kasuwanci, da kuma harba barkonon tsohuwa da bama-bamai kan mutane.

Kazalika sojojin na Isra’ila sun kuma kai hari kan ma’aikatan lafiya da ‘yan jarida.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: