Gwamna Aminu Masari yace baya jin daɗin kujerar gwamnan da ya ke akai saboda matsalar tsaro

0 181

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari yace baya jin daɗin kujerar gwamnan da ya ke akai saboda matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar musamman jihar sa.

Gwamnan a wata hira da yayi da gidan radio na DW Hausa, yace a kullum harkar mulki a Katsina tattare yake da kalubalen tsaro, kuma a kowane lokaci yana samun bayanai kan tsananin rashin tsaro daga kafofi da dama.

Masari ya bayyana cewa rashin tsaro ya kazanta ta inda har baya iya barci kuma baya jin daɗin hakan a matsayin shi na gwamna, saboda babu wani shugaba da yake kishin al’ummarsa da zai samu kwanciyar hankali a irin wannan yanayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: