Rundunar yansanda a jihar Imo ta samu nasarar hallaka wasu yan fashi guda biyu cikin gungun maahara da suka kai hari kan wasu al’uma.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Michael Abattam shine ya tabbatar da faruwar hakan a karamar hakumar Njaba dake jihar a safiyar yau misalin karfe 1:20.

Ya ce ayarin maharan dauke da makamai sunyi dirar mikiya a garin na Njaba domin kaddamar da harin kafin daga bisani dakarun kwantar da tarzoma na rundunar yan sandan su cimmusu.

Yace an samu bindiga kirar AK47 da jakar al’barusai da kuma mashin a wajen guda daga cikin wanda jamaian sukayi nasarar kashewa.

Kakakin ya bukaci mazauna yankin da su dawo gidajensu batare da wani dar-dar.

Ya yi bayanin cewa sumamen da jamian yan sandan suka kai an tsara shi ne don kawar da masu aikata laifuka a cikin gandun daji, sannan ya yi kira da goyon bayan mutane don cimma nasarar da ake bukata.

Abattam ya nemi su hanzarta kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa idan sun lura da wani baƙon mutum a cikin muhallinsu ko kuma duk wanda ke maganin raunin harsashi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: