Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira ga shugabanni da su guji rarrabuwar kawuna su kuma rungumi soyayya

0 69

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki na kabilar Ijaw da su guji rarrabuwar kawuna tare da yin aiki tare cikin soyayya da hadin kai don maslahar ‘yan kabilar Ijaw a Najeriya.

Jonathan ya yi wannan kiran ne lokacin da shuwagabannin kungiyar ta Ijaw ta kasa tare da rakiyar jami’an shiyya ta tsakiya na Majalisar Matasan Ijaw, suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Yenagoa, Jihar Bayelsa, jiya Juma’a.

Ya yi kira ga ‘yan kabilar Ijaw maza da mata da su sadaukar da kansu dan al’uma tare da sanya fifikon jama’a sama da muradan kai da kai, yana mai jaddada cewa bambance-bambancen da ke tsakanin Ijaw bai kamata ya kawo tsaiko ga haɗin kai ba.

Tsohon Shugaban kasar ya taya shuwagabannin kungiyar murnar nasarar da suka samu a zaben da suka gudanar, sannan ya yaba musu kan shirye -shirye da ayyukan da suke gudanarwa don inganta Ijaw.

Tun da farko, Shugaban kungiyar Farfesa Benjamin Okaba, ya nuna godiyarsa ga Jonathan saboda goyan bayan Gwamna Douye Diri don ganin an gudanar da babban zabe na ƙungiya mai zaman kanta, wanda aka bayyana  a matsayim sahihi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: