Kungiyar likitoci ta umarci mambobinta da su tsunduma yajin aikin gama gari a duka sassan kasar nan daga ranar litinin mai zuwa 2 ga watan agusta.

Umarnin hakan wanda aka fitar a yau biyo bayan ganawar shugabannin kungiyar da aka gudanar a Umuahia babban birnin jihar Abia.

Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman taron da ya gudana shugaban kungiyar Dr Okhuaihesuyi Uyilawa  yace bambobin kungiyar zasu tsunduma yajin aikin gama gari a fadin kasar nan.

Ya zayyana wasu daga cikin dalilan da yace shine abinda kungiyar ta Dogara dashi a matsayin hujjar zartar da wannan shawara, da suka hada da gazawar gomnatin tarayya wajen cimma bukatun da likitocin suka nema.

Shugaban kungiyar ya nemi afuwar yan Najeriya dangane da wannan mataki, wanda ya alakanta hakan da gazawar gomnati.

Idan dai zaa iya tinawa likitocin sun kauracewa guraren ayyukansu a watan afrilun daya gabata, inda suka bar marasa lafiya kwance batare da an dubasu ba a asibitocin gomnati.

Sun shafe kwanaki 10 daga bisani suka dawo bakin aikin bayan cimma yarjejeniya da gomnatin a wani taron ta bidiyon kai tsaye wanda aka kwashe sama da saoi 15 a ranar 10 ga watan afrilu.

Wasu daga cikin abubuwan da likitocin ke bukata gomnatin ta musu tun a wancan lokaci sun hada biyan su hakkokinsu na albashi akan kari.

Sun kuma bukaci karin Alawus da kashi 50 na albashi, tare da biyan aluwus na corona wanda suke bin gomnatin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: