Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ajiye kudurin sa na tsayawa takara

0 22

Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi ya bukaci tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya ajiye kudurin sa na tsayawa takara, domin ya mara masa baya, biyo bayan gogewar da yake da ita wajen ciyar da kasa gaba idan aka zabe shi a 2023.

Gwamna Jihar ta Bauchi, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels Tv ta cikin shirin ‘‘Politics Today’’ inda ya yi karin haske kan rikice-rikicen da jam’iyar PDP take ciki.

Tsohon Ministan na birnin tarayya ya bayyana cewa yana da gogewa ta fuskar ciyar da kasa gaba, sannan Matashi ne shi mai cike da koshin lafiya.

Haka kuma ya ce Abokan sa da kudancin kasar nan, sunyi alkawarin mara masa baya matukar ya samu tikitin tsayawa takarar.

Kazalika, ya ce goyan bayan da kungiyar Dattawan Arewa suka yiwa masa, baya nufin masu neman takara a Jam’iyar PDP a Arewa su tsaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: