Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, Ya Rusa Majalisar Kwamishinoninsa

0 177

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya rusa majalisar kwamishinoninsa, inda ya bukaci masu rike da mukamai daban-daban da su mika cikakkun bayanai kafin gobe.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai dauke da sa hannun Rabi’u Abubakar, a madadin ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Rabi’u Abubakar, wanda ya bukaci wadanda aka nada da su dauki matakin gaggawa akan wasikun da aka aika zuwa ga ofisoshin Babban Sakataren Gidan Gwamnati; da na Babban Sakatare a Ofishin Mataimakin Gwamna dake Gidan Gwamnati a Gombe; da Sakataren ofishin gwamnan jihar; da Magatakardar Majalisar Dokokin Jihar Gombe a Gombe; da Manyan Magatakardar a Babban Kotun Shari’a da Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunchi; da Dukkanin Manyan Sakatarori; da Dukkanin Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnati.

Ya bayyana cewa an yanke hukuncin ne saboda nasarar zaben da gwamnatin ta samu a zaben gwamna da aka gudanar kwanan nan, wanda ya kawo karshen gwamnatin Inuwa Yahaya ta farko.

Leave a Reply