JAMB Ta Kara Wa’adin Ranar Rufe Rijistar DE Ta Bana Da Mako Guda

0 78

Hukumar samar da guraben karatu a makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta kara wa’adin ranar rufe rijistar DE ta bana da mako guda.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya a Abuja ta hannun kakakin hukumar, Fabian Benjamin, bayan kammala taron shugabannin hukumar.

Fabian Benjamin yace rijistar jarabawar ta DE wacce aka fara a ranar Litinin, 20 ga watan Maris na bana, kuma aka tsara rufewa a ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilun bana, an kara mako guda, farawa daga ranar Juma’a, 21 ga watan Afrilun bana.

A cewarsa, an yi karin wa’adin a wani bangare na bayar da dama ga dukkanin wadanda suka mallaki takardar kammala makarantun gaba da sakandire kuma suka kasa samun nasarar yin rijistar saboda wasu matsaloli da suka shafi tantance sakamakonsu.

Yace hakan kuma zai bayar da dama ga sauran dalibai amma basu samu dama ba cikin lokacin da aka ware.

Leave a Reply

%d bloggers like this: