NCDC Ta Yi Rajistar Mutuwar Mutane 79 Da Jimillar Mutane 1,336 Da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Kwalara A Najeriya

0 76

Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa, NCDC, ta yi rajistar mutuwar mutane 79 da jimillar mutane dubu 1 da 336 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a kasarnan ya zuwa yanzu a bana.

Hukumar ta NCDC, a shafinta na intanet, ta bayyana hakan a cikin rahotonta na baya-bayan nan game da cutar kwalara.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, cutar kwalara cuta ce mai saurin kisa sakamakon kamuwa da kwayar cutar a cikin hanji.

Mutane na iya yin rashin lafiya lokacin da suka ci abinci ko shan ruwan da aka gurbata da kwayoyin cutar kwalara. A lokuta da dama cutar tana zuwa da sauki ba tare da wasu alamu ba, amma wani lokaci tana iya zuwa da tsanani kuma mai hadari ga rayuwa.

Hukumar ta ce kananan hukumomi 43 a fadin jihohi 12 ne suka bayar da rahoton bullar cutar, inda kididdigar wadanda suka mutu daga cikin wadanda suka rayu ya kai kashi 5.9 cikin 100. Hukumar ta ce jihohi 12n da suka samu rahoton bullar cutar a kasarnan sun hada da Abia, da Bauchi, da Bayelsa, da Cross River, da Ebonyi, da Kano, da Katsina, da Neja, da Ondo, da Osun, da Sokoto, da kuma Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: