Hukumar Kididdiga Ta Kasa, NBS, Ta Ce Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Karu Zuwa Kashi 22.04 A Shekara

0 77

Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 22.04 a shekara a watan Maris na bana.

Wannan dai ya zo ne a rahoton kididdigar farashi da hauhawar farashin kayayyaki na watan Maris na shekarar 2023 da aka fitar jiya a Abuja.

A cewar rahoton, adadin ya kai maki 0.13 bisa dari idan aka kwatanta da kashi 21.91 da aka samu a watan Fabrairun 2023.

Ya ce a shekara guda, adadin hauhawar farashin kayayyaki a watan Maris na 2023 ya kai kashi 6.13 bisa dari fiye da yadda aka samu a watan Maris na shekarar 2022 da kashi 15.92 cikin dari.

Rahoton ya ce gudummawar da kowane kaya ya bayar wajen hauhawar farashin sun hada da abinci da abubuwan sha da kashi 11.42 bisa 100 da gidaje, ruwa, wutar lantarki, gas da mai da kashi 3.69 cikin 100.

Sauran su ne tufafi da takalma da 0.69 bisa dari; kudaden sufuri da kashi 1.43 bisa dari; kayan katako, kayan aikin gida da na gyara da kashi 1.11 cikin dari da kayayyakin ilimi da kashi 0.87 bisa dari sannan sai kayayyakin lafiya da kashi 0.66 cikin dari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: