Gwamnatin Jigawa Tayi Rabon Tallafin Buhun Masara 1,160 A Kirikasamma

0 94

Gwamnatin jihar Jigawa ta bada tallafin buhunan masara 1,160 domin rabawa masu karamin karfi a yankin karamar hukumar Kiri-Kasamam.

Mataimakin shugaban karamar hukumar, Malam Al`asan Mattafari shine ya kaddamar da rabon masarar amadadin shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Garba Kubayo.

Ya shawarci kansilolin yankin zababbu da nadaddu su tabbatar da yin gaskiya da adalci wajen rabon masarar.

Yace za`a raba masarar ga akwatunan zabe na karamar hukumar guda 116, inda kowane akwati zai sami buhu goma.

Malam Al`asan Mattafari ya yabawa gwamna Muhammad Badaru Abubakar bisa kokarinsa na inganta rayuwar al`umma.

A wani cigaban kuma gwamna Badaru, yace akwai yuwuwar adadin masu dauke da cutar Corona a jihar yakai mutum 800, kamar yadda kwararru sukayi kiyasi, karkashin tsari mai inganci.

Da yake ganawa da yan jaridu a garin Dutse babban birnin jihar a jiya laraba, yace muddin ba’a dauki matakin da ya dace ba wajen yakar cutar corona ba, akwai yuwuwar adadin zai iya kaiwa mutum 20,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: