Tufka Da Warwara: Gwamnoni Sun Bukaci Majalisa Ta Dakatar da Wani Kuduri

0 68

Kungiyar gwamnonin kasarnan ta bukaci majalisar tarayya, da ta dakatar da kudirin dokarnan kan cutuka masu yaduwa, domin samun damar tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

Haka kuma ta kafa wani kwamati mai mutum 3, da ya hadar da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, sai gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, da kuma na Plateau Simon Lalong, da zai gana da shugabancin majalisar a kan batun.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun  shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, bayan taron kungiyar kan Covid-19 karo na 8, da ya gudana ta kafar Video a jiya Laraba.

Da suke bayyana damuwa dangane da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar corona a kasarnan, gwamnonin sun cimma matsaya wajen hada hannu da gidauniyar Dangote, bayar da horo na musamman ga ma’aikatan lafiya na sa kai, da kuma samar da karin cibiyoyin killace masu cutar.

Kazalika sun amince da samar da karin wuraren ajiya, domin tara kayayyakin tallafi da kamfanoni masu zaman kansu suka bayar da gudunmawa, a kokarin isar da tallafin ga mabukata a kowace jiha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: