Gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar yara 14 sakamakon barkewar cutar kyanda a kananan hukumomi tara na jihar

0 87

Gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar yara 14 sakamakon barkewar cutar kyanda a kananan hukumomi tara na jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Afam Obidike ne ya sanar da hakan a yau a wani taron manema labarai a Awka, babban birnin jihar.

Ya ce a kalla mutane 414 ne suka kamu da cutar kyanda a kananan hukumomi tara na jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa tallafin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) suka bayar sun taimaka wa jihar wajen dakile yaduwar cutar.

Ya ce a wani mataki na shawo kan cutar, an yi wa yara dubu 19 da 609 wanda ba a musu allurar ba daga jarirai zuwa ‘yan watanni 59.

Kwamishinan ya ce an kuma yi wa al’ummar da ke kewaye da kananan hukumomi tara allurar rigakafin kamuwa da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: