Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da kashi na biyu na rigakafin Korona

0 75

Gwamnatin jihar Bauchi a jiya ta kaddamar da kashi na biyu na rigakafin COVID 19 tare da allurai dubu 100,296 a kananan hukumomi 20 na jihar.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jihar kuma mataimakin gwamnan jihar Bauchi Sanata Baba Tela, ya bayyana hakan yayin kaddamar da atisayen rigakafin cutar karo na biyu a Bauchi.

Ya ce jihar ta karɓi allurai 100,296 na allurar COVID-19 daga gwamnatin Amurka don yin allurar rigakafi ga jama’a a ƙananan hukumomi 20.

A cewarsa, gwamnatin jihar kuma tana jiran sauran alluran rigakafi daga Pfizer da Johnson Johnson don su cika kashi na farko da aka karɓa daga gwamnatin Amurka.

Tun da farko, shugaban hukumar bunkasa kiwon lafiya matakin farko na jihar Bauchi Dr Rilwanu Mohammmed ya ce hukumar za ta kara himma don ganin an yiwa kowa allurar rigakafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: