Gwamnatin Jihar Edo Ta Kara Mafi Karancin Albashin Ma’aikata A Jihar Daga Naira 30,000 Zuwa 40,000

0 111

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da gwamna Godwin Obaseki ya fitar jiya.

Gwamnan na jihar Edo ya kuma sanar da rage kwanakin aiki daga biyar zuwa uku, yayin da mazauna jihar ke ci gaba da kokawa kan illar cire tallafin man fetur.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tallafawa ma’aikata a cikin wannan rayuwa da ake ciki mai matukar wahala. Gwamna Godwin Obaseki ya kuma ce gwamnatin sa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta magance wahalhalun da mazauna yankin da jihar ke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: