Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Honorabul Tasiu Maigari A Jiya Ya Sanar Da Rusa Majalisar Ta Bakwai

0 106

Tasiu Maigari, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan gabatar da jawabinsa na karshe, ya bayyana mambobin majalisar ta 7 a matsayin daya daga cikin mafi kwazo da aka taba samarwa a jihar.

Kakakin majalisar ya kuma yabawa tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari bisa goyon bayansa da shawarwarinsa da kuma hadin kai ga majalisar ta bakwai.

Tasiu Maigari ya bayyana cewa a cikin shekaru hudun da suka gabata an zartar da kudirorin doka guda 54 a majalisar ta 7.

Ya kuma kara da cewa kimanin wasu kudurori 324 ne aka zartar kuma bangaren zartarwa ya aiwatar da 74 daga cikin su. Wasu daga cikin kudirorin da kakakin majalisar ya bayyana sun hada da dokar hukumar majalisar dokokin jihar Katsina, da dokar nuna wariya ga nakasassu, da dokar inganta shigar da yara zuwa makarantun firamare da kuma batutuwa masu alaka, da dokar daidaita kudaden shiga, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: