Gwamnatin Jigawa na Duba Yiwuwar Tashin Garin Daƙayyawa a Karamar Hukumar Kaugama

0 250

Gwamnatin Jihar Jigawa na duba yiwuwar tashin garin Dakayyawa a Karamar Hukumar Kaugama, a mayar da shi zuwa wani waje daban mai tudu, sanadiyyar iftila’in ambaliyar ruwan dake abbadar garin duk shekara.

Ya zuwa yanzu dai, Kananan Hukumomi 3 ne a nan jihar ta Jigawa, ambaliyar ruwan ta shafa a bana.

Ambaliyar tayi awon gaba da gidaje da gonakin mutane, biyo bayan mamakon ruwan sama da kuma tumbatsar kogin Hadejia, a Kananan Hukumomi 3 da abin ya shafa. Kananan Hukumomin sune Miga da Kaugama da kuma Guri.

Sai dai, ba a samu asarar rai ba, amma wasu mutane da ambaliyar ta shafa, kuma suka rasa gidajensu, an tsugunnar dasu a cikin makarantun firamare.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Umar Namadi, shine ya bayyana cewa akwai yiwuwar tashin garin na Dakayyawa, yayinda ya ziyarci Kananan Hukumomin da ambaliyar ta shafa domin binciken gani da ido.

Yace gwamnati mai ci, na aiki tukuru, domin lalubo bakin zaren ambaliyar ruwa dake aukuwa a jihar duk shekara.

Alhaji Umar Namadi, tunda farko, sai da ya umarci hukumar agajin gaggawa ta jiha (SEMA), data tallafawa wadanda suka gamu da iftila’in, da kayayyaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: