Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da hakumar kare makarantu da cibiyoyin gwamnati

0 133

A wani yunkuri na tabbatar da tsaro a makarantun jihar Jigawa, gwamnatin Umar Namadi ta kaddamar da hakumar kare makarantu da cibiyoyin gwamnati.

Sawaba radio ta bayar da rahotan cewa an kaddamar da rundanar tsaron makarantun ta masu ruwa da tsari a baya-bayan nan a Dutse, wanda aka gudanar domin matsalolin rashin tsaro a fadin makarantun jihar Jigawa.

Sabuwar rundanar, wanda zaka lakume naira miliyan 342, zata ria sanya idanu a gine-ginen gwamnati da sauran kadarori.

Da yake jawabi wajen bikin kaddamarwar gwamna Umar Namadi ya tabbatar da muhimmancin tsare tsare makarantun domin samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa a tsakanin dalibai.

Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa sun dauki matasa dubu 10 aikin a wani yunkuri na cimma muradin da kuma samar da ayyukan yi a tsakanin matasa.

Leave a Reply