Gwamnatin jihar jigawa ta maida dukkanin kafafan yada labaranta zuwa masu aiki na,urorin zamani kamar yadda ma,aikatar yada labarai ta tarayya ta bada umarni.

Gwamna Mohammad Badaru Abubabkar ya bayyana haka a taron kungiyar ma,aikatan kafafan yada labarai ta kasa shiyyar arewa maso yamma.

Alhaji Badaru Abubakar yayi bayanin cewa muhimmanci kafafan yada labarai wajen isar sakon allaumma ga gwamnati kokuma sakon gwamnati ga Al,umma.

Haka zalika gwamnan ya sanar da cewa jihar jigawa ce zata karbi bakuncin babban taron kungiyar na kasa daza a gudanar anan gaba.

Daganan yayi kira da masu hannu da shuni su zuba jari a fannain sadarwa ta hanyar bude kafafan yada labarai masu zaman kansu.

Kazalika gwamnatin jiha na biyan alawus alawus na mussaman ga yanjaridun suke aiki a kafafan yada labaranta domin basu kwarin gwiwar gudanar da aiyyukansau yadda ya kamata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: