Gwamnatin jihar Jigawa ta mika gudummawar motoci kirar Toyota camry guda 4 ga Jami’ar Fasaha ta gwamnatin Tarayya da ke Babura

0 82

Gwamnatin jihar Jigawa ta mika gudummawar motoci kirar Toyota camry guda hudu ga jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Babura.

Da yake mika motocin ga mahukuntar jami’ar, kwamishinan ilimi Kimiyya da fasaha na jiha, Dakta Lawan Yunusa Danzomo ya ce gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya umarci ma’aikatar da ta mika motocin ga jami’ar domin tallafawa wajen fara karatu a jami’ar kamar yadda ya kamata.

Kwamishinan ya umarci shugabannin jam’iar da suyi aiki tukuru wajen tabbatar da cikar manufofin kafa jami’ar.

A jawabinsa mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Sabo Ibrahim Birnin Kudu, wanda ya jagoranci shugabannin zuwa wajen karbar motocin, ya godewa Gwamna Badaru Abubakar bisa bayar da fili mai fadin kadada 600 domin gina sansanin jami’ar na dindindin, kari bisa motocin guda hudu.

Ya sanar da cewa za a fara harkokin koyo da koyarwa a jami’ar nan da watan Satumba mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: