Hukumar Alhazai ta kasa ta bayyana cewa ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta gaza biyan bukatar data mika na a karawa Najeriya yawan kujerun aikin Hajjin bana

0 86

Hukumar Alhazai ta kasa ta bayyana cewa ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta gaza biyan bukatar data mika na a karawa Najeriya yawan kujerun aikin Hajjin bana.

An bayar da labarin cewa hukumomin Saudiyya sun baiwa Najeriya kujerun alhazai dubu 43 da 8, sabanin kujeru dubu 95 da aka baiwa kasar a shekarar 2020.

Wata sanarwa da mataimakiyar daraktan hulda da jama’a ta hukumar alhazai ta kasa Fatima Sanda-Usara ta fitar ta ce kwamishinan ayyuka na hukumar alhazai ta kasa Abdullahi Magaji Hardawa ya jagoranci wata tawaga domin mika bukatar neman karin amma abin ya ci tura.

A cewar sanarwar, bukatar ta zama dole domin a rage kukan da masu gudanar da aikin hajji masu zaman kansu ke yi dangane da karancin kujerun da aka samu.

A saboda haka hukumar ta bayar da harkuri ga masu gudanar da aikin hajjin da basu ji dadin rashin samun karin ba, inda ta roke su da su karbi lamarin a matsayin kaddara, tare da sa ran samun dama ta gaba a shekara mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: