Hukumar kidaya ta kasa ta shirya domin gudanar da aikin kidayar gwaji daga ranar 11 zuwa 24 ga watan gobe a wasu kananan hukumomi 9 da aka zaba a jihar Jigawa

0 57

Hukumar kidaya ta kasa ta shirya tsaf domin gudanar da aikin kidayar gwaji daga ranar 11 zuwa 24 ga watan gobe a wasu kananan hukumomi 9 da aka zaba a jihar Jigawa.

Aikin kidayar gwajin ya hadar da kidaya gidaje da tantance yankunan kidaya da kuma kidaya mutane dake kowane gida a wuraren da za a gudanar da aikin.

Da yake jawabi lokacin bude bitar bada horo ga jami’an da zasu gudanar da aikin, kwamishinan hukumar a jihar Jigawa, Garba A.G Zakar ya jaddada kudirin hukumar wajen samun nasarar aikin kidayar ta kasa dake tafe ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Ya ce an zabo jami’an gudanar da aikin kidayar ne da masu dubawa da jami’an kula da aikin su 104 daga kananan hukumomin da aikin kidayar gwajin zai gudana.

Kananan hukumomin da aka zaba domin gudanar da kidayar gwajin sune Birnin Kudu da Dutse da Miga da Malammadori da Birniwa da Maigatari da Babura da kuma Kazaure.

Leave a Reply

%d bloggers like this: