Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya hannu kan dokar hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da fyade ga kananan yara

0 43

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanya hannu kan dokar kare mutumcin Yara kanana wanda zata rika yankewa mutanen da suka yiwa Yara kanana fyade hukuncin kisa ba tare da zaman gidan Yari ba.

Kwamishinan Ma’aikatar Shari’a Kuma Babban Lauyan Gwamnati Dr. Musa Adamu Aliyu, shine ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Dutse.

A cewarsa, duk wanda Kotu ta same shi da laifin yiwa yara kanana yan kasa da shekara 10 fyade, za’a yanke masa hukuncin kisa, ba tare da zaman gidan Yari ba.

Kwamishinan, ya ce Gwamna Badaru Abubakar a farkon wannan shekara, ya sanya hannu kan dokar hukunta duk wanda aka samu da laifin fyade ta hanyar daurin rai-da-rai ko kuma hukuncin kisa.

Sai dai ya ce bayan Gwamnan ya sake sanya hannu kan sabuwar dokar kare hakkin Yara kanana, wanda ta kunshi cewa daga yanzu duk wanda aka samu da laifin yiwa yar kasa da shekara 10 fyade za’a yanke masa hukuncin kisa.

Dr. Musa Adamu Aliyu ya ce Ma’aikatar sa, ta samu korafe-korafen cin zarafin yara 196 inda ta samu nasarar gabatar da 178 a gaban Kotu domin neman fassarar Doka.

Haka kuma ya koka kan yadda ake samun tsaiko a fannin Sharia wajen yanke hukuncin fyade, inda ya kara da cewa hakan yana daga cikin Kalubalan da Jihar Jigawa take fuskanta, sai dai ya ce abu ne da ya shafi kasar nan gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: