Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane.

0 239

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa taka hoton kwankwaso da gwamna Ganduje yayi ba dagangan bane kuma ba shiryayyen abu bane.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, shine ya faɗi haka, yace hoton da ake yaɗawa na gwamna Ganduje yana taka Fastar kwankwaso a wajen taron APC da ya gudana ranar Asabar, ba da sanin mai girma gwamna bane.

Kwamishinan ya ƙara da cewa kowane irin banbancin siyasa ke tsakanin mutanen biyu, ba halayyar gwamna Ganduje bane yayi irin wannan abun ga wani ɗan siyasa.

Yace yayin da ake cigaba da yaɗa hotunan, har wasu sun fara sukar gwamna akan lamarin saboda wata manufar su ta siyasa, lamarin zai iya zama wata babbar matsala idan ba’a fito an bayyana gaskiya ba.

Malam Garba yace kowa yasan gwamna Ganduje da son zaman lafiya da girmama mutane, bai kamata ace ana sukar sa kan abinda yayi bada saninsa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: