Labarai

Gwamnatin jihar Neja ta karyata ikirarin da ta yi na cewa wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya NAF ya kashe kananan yara 6

Gwamnatin jihar Neja ta karyata ikirarin da ta yi na cewa wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya NAF ya kashe kananan yara shida.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ya fitar jiya a birnin Minna, inda ya karyata labarin da ake yadawa cewa, shine ya tabbatar da mutuwar yaran, kamar yanda wasu kafafen yada labarai na yanar gizo ke yadawa.

Ya kuma caccaki rahoton da wata jarida ta yanar gizo wacca ta buga inda ya bayyyana yadda aka kashe yaran shida, yana mai jaddada cewa bai taba yin irin wannan hirar da wata kafar yada labarai ba.

A cewar Matane, rahoton na karya, ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da wannan labaran.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: