Dalilan da yasa wasu matasa suka yi cincirindo tare da nuna goyan bayan su akan takarar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben 2023

0 18

Wasu matasa maza da mata a Safiya yau sunyi cincirindo tare nuna goyan bayan su akan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Matasan sun isa ofishin tsohon shugaba ne dake Maitama a Abuja, akan wasu manyan motoci 4 dauke da kwalaye suna rokan sa daya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

Sun kuma bazu a wasu titunan Abuja dauke da  kwalaye  masu rubutu dake nuna goyan bayansu akan tsohon shugaban ya amince da manufarsu.

Yayin dayake jawabi ga matasan Goodluck Jonathan, yace har yanzu da sauran lokaci kafin ya yanke shawarar fitowa ko kuma akasin haka.

Ya kuma godewa matasan bisa ziyarar da suka kai masa tare da nuna goyan su akan sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: