Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan kasuwa da masu zuba jari da su rika amfani da dabaru da albarkatu a fannonin tattalin arziki wanda zaiyi tasiri na dogon lokaci wajen samar da ayyukan yi da rage radadin talauci.

Shugaban, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote, da mambobin kungiyar a fadar shugaban kasa dake Abuja, a yau Juma’a, ya bada tabbacin cewa gyara ababen more rayuwa shine Babban abinda gwamnatin sa ta maida hankali akai.

Shugaban ya ce kalubalen da ke tattare da sufuri da makamashi za su ci gaba da jan hankalin jama’a don samun sauyi.

Don haka ya bukaci ‘yan kasuwa a kasar nan da masu zuba jari na kasashen waje da su mai da hankali kan bangarorin da za su taimaka wajan kawo sauyi.

Buhari ya yabawa Dangote kan yadda yake saka hannun jari a duk fannonin da ke kawo wa gwamnatin tarayya babbar riba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: