Wani fashewar bam ya kashe mutum 5 a wata mashaya a Jihar Taraba

0 63

Wani harin bam da aka kai a wata mashaya da ke Jihar Taraba a gabashin Najeriya ya kashe aƙalla mutum biyar.

Wasu 19 sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani abu a garin Iware.

Shaidu sun ce an ɓoye bam ɗin ne a cikin wata jaka.

Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Talata yayin da mutane suka taru a majalisar da ake shan barasa.

Rundunar ‘yan sandan jihar sun shaida wa BBC cewa ɗaya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin ya mutu, amma ba a sani ba ko ɗan ƙunar-bakin-wake ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: