Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a da Litinin masu zuwa a matsayin ranakun hutu domin bikin easter.

Bikin na easter biki ne da mabiya addinin kirista ke tunawa da tashin Yesu Almasihu bayan an gicciye shi.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shine ya sanar da hutun cikin wata sanarwa da aka fitar yau a madadin gwamnatin tarayya.

Cikin sanarwar wacce babban sakataren ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore ya fitar a madadinsa, ministan ya bukaci mabiya addinin kirista su yi koyi da sadaukarwa da hadin kai da yafiya da kirki da kauna da zaman lafiya da hakuri, wadanda Yesu Almasihu ya koyar.

Aregbesola ya kuma yi kira ga mabiya addinin kirista da sauran ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bikin na easter na bana su yi addu’o’in kawo karshen dukkan kalubalen tsaron da ya addabi kasarnan.

Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za tayi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa ta kawo karshen dukkan hare-haren batagari.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: