Yayin da zabukan shekarar 2023 ke kara karatowa, gwamnatin tarayya ta nanata cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta zama ba, kuma baza ta zama barazana ga kafafen yada labarai ba.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayar da wannan tabbaci yau a Abuja lokacin da wata tawaga daga cibiyar yada labarai ta duniya reshen Najeriya ta kai masa ziyara.

Ya ce Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka fi ‘yancin fadin albarkacin baki a duniya kuma gwamnati ba ta shirin tauye ‘yancin ‘yan jarida ko tauye wa kowa ‘yancinsa.

Lai Mohammed ya ce ya ji dadin yadda kungiyoyi masu mahimmanci irin su Cibiyar Yada Labarai ta Duniya ke daukar batun ’yancin aikin jarida da muhimmanci.

Tun da farko, shugaban tawagar, Musikilu Mojeed, ya ce sun zo ma’aikatar ne domin duba yadda za su hada kai don ganin Najeriya ta samar da kyakkyawan yanayin gudanar da aikin jarida, musamman ganin kakar zabe ta 2023 ta gabato.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: